Kiwon Lafiya
Shekarun baya Sarakunan Saudia na zuwa Najeriya don a duba lafiyar su inji Ministan lafiya
Karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce kasar nan ta amfana matuka tare da samun kudin shiga ta hannun masu zuwa a duba lafiyar su a kasar nan.
Jaridar Punch ta rawaito karamin ministan, ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja, inda ya ce a baya ‘yan kasashen duniya da dama, sun amfana da zuwa duba lafiyar su a shekarun baya.
Mamora ya kara dacewa, a shekarun alif dari tara da hamsin da kuma alif dari tara da sittin, kasar nan ta samu kudin shiga sosai inda hatta masu rike da madafun iko, wato Sarakunan kasar Saudi Arabia, suna zuwa akai-akai don duba lafiyar su a Asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan.
Karin labarai:
Zamu fito da sabbin dabaru na yaki da cutar lassa- Ministan lafiya
Gwamnatin Kano za ta fara karrama ma’aikatan lafiya
Kamafanin dillancin labarai na kasar nan, ya ruwaito ministan na cewa mutane na tafiya kasashen ketare duba lafiyar su, sakamakon rashin kwararru da kuma kayan ayyuka na zamani kuma sabbi.
Don haka ya zama wajibi a gare mu, da mu samar da kayan aiki tare da jami’ai kwararru don rage tafiya kasashen ketare neman magani.
Hakkin mu ne akan kasar nan, da mu samar da ingantattun kayan aikin lura da lafiya, don samar da lafiya ga al’ummar kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login