Labaran Wasanni
Shin ko Atletico Madrid za ta samu nasara kan Liverpool?
Tun daga lokacin da kungiyar kwallon kafa ta Atlentico Madrid dake kasar Spaniya ta samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun turai wato Champions league kungiyar ke fuskantar kalubale na rashin nasara a wasanninta.
Atletico Madrid dai ta doke Liverpool a wancan lokacin a filin wasanta na Wanda-Metropolitano a gasar cin kofin zakarun turai ta Champion league.
Kafin wasan kungiyar ta Liverpool tayi wasanni arba’in da biyu ba’a samu nasara a kanta ba.
Haka kuma ta shafe wasanni ashirin da shida a gasar cin kofin premier ta kasar Ingla ba tare da an ci ta wasa ba wanda hakan ya sanya ta baiwa mai biye mata a gasar Manchester city tazarar maki ashirin da biyu.
Tun daga lokacin da tawagar ‘yan wasan ta Diego Simeone wato Atletico Madrid ta samu nasara kan Liverpool din, kungiyar kwallon kafa ta Watford dake kasar Ingila ta kawo karshen samun nasara kan Liverpool a gasar Premier din kasar bayan da ta samu nasara a kanta da ci uku mai ban haushi.
Ko a satin da ya gabata ma, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa kungiyar kwallon kafar ta Liverpool, inda ta zura mata kwallaye biyu da nema, hakan ya sa kungiyar Liverpool ta yi rashin nasara a wasanni uku sannan aka zura mata kwallaye shida.
A bara dai kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ce ta samu nasarar lashe gasar Champions league bayan da ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ita ma daga kasar ta Ingila da ci 2-0.
A ranar talata mai zuwa ne Liverpool za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a filin wasa na Anfield a wasa zagaye na biyu na kofin zakarun turai inda a wasan ne za a tabbatar da kungiyar da za ta zagaya zuwa zagaye na gaba a gasar.
You must be logged in to post a comment Login