Rahotonni
Rahoto : Shirin bada ilimi kyauta na Ganduje ba zai tabbata ba sai ya yi tafiya da kungiyoyi – RUMFOBA
Kungiyar tsofaffin daliban kwalejin Rumfa ta kasa ta ce shirin bayar da ilimi kyauta kuma wajibi na gwamnatin jihar Kano ba zai tabbatar ba har sai ta yi tafiya da kungiyoyin tsofaffin dalibai da kuma malamai.
sakataren kungiyar Malam Garba Usman Garba ne ya bayyana hakan yayin taro tsofaffin daliban makarantar na ‘yan ajin shekarar 2000, da suka gudanar da bikin cika shekaru 20 da kammala makarantar.
Ku saurari rahoton a wakiliyarmu Aisha Shehu Kabara cikin jerin rahotonnin mu.
Ga ƙarin bayani cikin Rahoton Aisha Kabara :
Garba Usman Garba ya ce tsoffin dalibai suna da rawar takawa domin samun nasarar wannan cimma wannan kyakkyawar aniya ta gwamnatin Jihar Kano, kasancewarsu cikin wadanda suka rayu a makarantar.
Ya kara da cewa a irin wannan taro ne ake gane wadanda suke bukatar tallafi a tsakanin tsofaffin daliban, inda ya tabbatar da cewa suna kokarin tallafawa junansu da kuma makarantunsu.
Shehu Yahaya Shehu shi ne mataimakin shugaban kungiyar ta RUMFOBA ajin shekarar 2000, ya ce a wananan shekarar suna bikin murnar cikarsu shekara 20 da kammala makaranta da kuma kasancewar su daliban da suka fara rubuta jarrabawar ta NECO a kasa baki-daya.
Shi ma mai magana da yawun kungiyar Jamilu Shehu Kabara, ya ce za su ci gaba da tallafawa makarantar da kayan koyo da koyarwa tare da kiran tsofaffin dalibai da su rungumi dabi’ar tallafawar.
A yayin taron an gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login