Labarai
Sarki Muhammadu Sanusi II ya kammala Hawan Sallar Gani na kwanaki 2

Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya kammala hawan sallar gani na kwanaki biyu inda ya kewaya sassa daban daban na birnin Kano domin nuna murnar bukukuwan maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sarkin ya shirya wannan hawa ne domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW, wanda ya kasance karo na farko a tarihin Masarautar Kano.
Hawan na bana ya samu halartar ɗaruruwan manyan mutane da kuma dandazon matasa maza da mata da dayyawa, waɗanda suka fito domin nuna farin cikinsu da Mai Martaba.
A Yayin hawan dai Mai Martaba sarkin ya cigaba da yi wa al’umma addu’o’i, musamman zaman lafiya haɗin kai da kwanciyar hankali a Kano da Najeriya baki ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login