Connect with us

Labarai

Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi II ya kammala Hawan Sallar Gani na farko

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya kammala hawan Sallar Gani na kwanaki biyu da ya gudanar a sassa daban-daban na birnin Kano, domin nuna murnar bikin Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Hawan Sallar Gani na bana ya gudana ne a matsayin wani bangare na bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW, kuma an bayyana shi a matsayin karo na farko da aka gudanar da irin wannan hawa a tarihin Masarautar Kano.

A tsawon kwanaki biyun, Mai Martaba Sarkin ya kewaya sassa daban-daban na birnin Kano, inda ɗaruruwan manyan mutane da dubban al’umma, musamman matasa maza da mata, suka fito domin tarbar Sarkin da nuna farin cikinsu.

Wakilinmu na Masarautar Kano, Shamsu Dau Abdullahi, ya rawaito cewa yayin hawan, Mai Martaba Sarkin ya yi ta yi wa al’umma addu’o’in samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!