Connect with us

Labarai

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya bukaci a warware rikicin Habasha ta hanyar tattaunawa da Diflomasiyya

Published

on

Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya yi kira da a warware rikicin ƙasar Habasha ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya, maimakon amfani da ƙarfin soja.

 

Shugaba Al-Sisi ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin El-Alamein na ƙasar Masar, inda ya yi gargaɗin cewa rikicin na iya yaɗuwa zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da Habasha, matuƙar ba a ɗauki matakan shawo kansa ba.

 

Shugaban na Masar ya kuma gana da takwarorinsa na Eritrea, Somaliya da Sudan, inda suka tattauna kan hanyoyin da za a bi domin dakile yaɗuwar rikicin, musamman a yankunan da ke kan iyakokinsu da Habasha.

 

A jawabinsa, Abdel Fattah al-Sisi ya yi Allah-wadai da abin da ya kira katsalandan ɗin ƙasashen waje a harkokin cikin gida na ƙasashen Afirka, yana mai cewa ya kamata dangantaka tsakanin ƙasashen ta ginu bisa mutunta juna da fahimtar juna, ba barazana ko tsoma baki ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!