Labarai
Yawan amfani da Intanet na karuwa fiye da yadda a ke fadada hanyoyin sadarwa- NCC

Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC, ta ce yawan amfani da Intanet a kasar na karuwa fiye da yadda a ke fadada hanyoyin sadarwa, lamarin da ke kara matsin lamba kan kayayyakin sadarwa.
NCC ta ce Najeriya ta yi amfani da kusan Terabytes miliyan 1.6 na bayanan Intanet a watan Yulin bana, wanda ke nuna karuwar kusan kashi 47 cikin 100 cikin shekara guda.
Hukumar ta kuma ce duk da cewa kashi 90 cikin 100 na ‘yan Najeriya na da damar amfani da hanyoyin sadarwar wayar salula, kusan kashi 27 ne kawai ke da wayoyin zamani, yayin da yawan shigar intanet ya kai kashi 57.4 cikin 100.
Ta ce tsadar wayoyin zamani, karancin ilimin amfani da fasahar zamani da kuma rashin wadataccen wutar lantarki na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban sadarwa, tare da bukatar karin zuba jari a bangaren.
You must be logged in to post a comment Login