Ƙetare
Shugaba Biden ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara
Shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2024, tare da yin shirin sake fafatawa da tsohon shugaban kasar Donald Trump.
BBC ta ruwaito cewa, an yi tsammanin jam’iyyar Democrat za ta sake neman wa’adi na biyu na shekaru huɗu tare da kaddamar da yakin neman zaɓensa a wani hoton bidiyo a ranar Talata.
Shugaban ya ce, wannan muhimmin lokaci ne da zai sake bayyana aniyrasa ta sake mulkar Amurka.
Mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Harris, mai shekaru 58, ita ta nuna aniyar sake zama abokin takararsa.
Mista Biden, mai shekaru 80, shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a tarihin Amurka, kuma da alama zai fuskanci tambayoyi kan shekarunsa a tsawon lokacin yakin neman zaɓe.
Zai kasance yana da shekara 86 bayan kammala wa’adinsa na biyu a kan mulkii a 2029.
You must be logged in to post a comment Login