Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci malaman makarantu su kasance jakadu na gari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci malaman makarantun kasar nan da su kasance jakadu na gari a ko ina, kasancewar hakan zai taimaka wajen inganta karatun yara da kuma cigaban kasar nan.
Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a yayin taron ranar bikin malaman makarantu ta duniya, wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja, mai taken ‘yancin samun ilimi na da nasaba ne da ingantattun malaman makarantu.
Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yace kasancewar yara sune manyan gobe, suna da irin tasu muhimmiyar rawar da zasu iya takawa wajen ciyar da kasar nan gaba, a saboda haka akwai bukatar a samar da gogaggun malaman da zasu koyar da su a makarantu.
Ya kara da cewa duk da cewa aikin koyo da koyarwa na fuskantar kalubale a Najeriya, musamman ma bangaren albashi, rashin mutun ta kai da kuma rashin isassun malamai hadi da rashin horas da su, amma hakan be hana gwamnati mayar da hankali wajen tabbatar da ingancin malaman makarantu ba.
Shugaba Buhari ya lura da cewa matsawar ana bukatar samun cigaba mai dorewa daga nan zuwa shekarar 2030, akwai bukatar ma’aikatar ilimi ta tarayya ta samar da wasu sauye-sauye da zasu inganta tsarin koyo da koyarwa a makarantun kasar nan.
Shugaba Buhari yayi kira da a inganta tsarin koyo da koyarwa, inda ya bukacia malaman makarantun kasar nan da su tabbatar cewa sun samu lasisin shedar aikin malanta daga hukumar rijistar malamai ta kasa, kafin wa’adin karbar sa ya kare a karshen shekarar 2019.