Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya bukaci yan Najeriya da su yi amfani da darussan wata Ramadana wajen kyautatawa juna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da darussan da ke cikin azumin watan Ramadan domin kara kusantar Ubangiji da soyayyar juna da taimakekeniya da kuma tausayawa na kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja.
A cikin sakon taya al’ummar musulmi murnar fara azumin na watan Ramadan din shugaban kasar ya yi kira ga al’ummar musulmi da su yi addu’a ga kasar nan.
Ta cikin sanarwar dai shugaba Buhari ya kara da cewa, manufar azumi ba wai kauracewa abinci ko abin sha bane kawai, lokaci ne da al’ummar musulmi ya kamata su tsarkake kansu daga aikata munanan laifuka.
Shugaban kasar ya kuma bukaci al’ummar musulmi a duk duniya baki daya da su yi koyi da kyawawan halaye irin na Annabi Muhammadu sallalahu alaihi wasallam.