Labarai
Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a yau
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagorantci taron majalisar zartaswa ta kasa a yau Laraba, wanda aka gabatar ta kafar Internet.
Kafin fara taron sai da mahalratrsa suka don gudanar da adduo’i na musamman don karrama wasu tsofaffin ministoci biyu da suka rasu a baya-bayan nan.
Tsofaffin ministocin sun hada da: Rear Admiral Olufemi Olumide da kuma Manjo janar Sam Momah.
Marigayi Olumide dai ya taba ya rike mukamin kwamishinan sufuri da ayyuka na tarayya a zamanin mulkin Yakubu Gawon da kuma Murtala Muhammad, yayin da Marigayi Sam Momah ya taba rike mukamin ministan ilimin kimiyya da fasaha a lokacin shugabancin marigayi janar Sani Abacha.
Cikin ministocin da suka hallara a zauren majalisar sun hada da, Ministan kudi kasafi da tsare tsare Hajiya Zainab Ahmad da ministan tama da karafa Sanata Olamilekan Adegbite da kuma Attoni Janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami.
Sauran sun hada da Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad da ministan lafiya Dr Osagie Ehanire da Adeleke Mamora da kuma ministan Muhalli, Alhaji Muhammad Mahmud.
You must be logged in to post a comment Login