Labarai
Shugaba Buhari ya yi ganawa ta Internet kan rikicin Mali da kungiyar ECOWAS
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci zaman da shugabannin kungiyar bunkasa tattalin yammacin Afrika ECOWAS ke yi don lalubo hanyoyin sasanta rikicin kasar Mali.
Shugaba Buhari ya halarci zaman na yau ta kafar Internet a fadar sa da ke Villa a Abuja.
A yayin zaman na yau, wanda shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Jamhuriyar Niger Mahmadou Issoufu ke jagoranta.
Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar ta yi zama tun bayan da sojoji suka hambarar da zababban shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.
Tun da fari dai, Sojojin da suka karbe mulki sun bayyanawa jakadan ECOWAS a kasar mali kuma tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan da sauran wakilan kungiyar ta ECOWAS cewa suna bukatar shekrau uku kafin mika mulki ga hannun zababbiyar gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login