Labarai
Shugaba Buhari yayi tsokaci a Karo na farko kan batun zargin gwamnan Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karon farko ya yi tsokaci kan batun nan na zargin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar nagoro a hannun ‘yan kwangila, inda ya ba da tabbacin daukar matakin da ya dace.
Tsokacin na shugaban kasa na zuwa ne a dai dai lokacin da wani dalibi ‘dan asalin Kano da ke kasar Faransa ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan ta yi koyi da gwamnan na Kano wajen biyan dalibai kudaden tallafin karatu da sauransu.
Sai dai a karon farko cikin yanayin da ba a saba gani ba, shugaba Buhari ya tambayi daliban shin ko sun yi tozali da wani Faifan bidiyo da ake zargin gwamnan na Kano na karbar nagoro a hannun ‘yan kwangila.
Shugaba Buhari ya shaida cewa sun mikawa jami’an tsaro Faifan bidiyon don nazarta tare da fadada bincike, kuma tabbas za a dauki matakin da ya dace matukar aka samu gwamnan da laifi a kai.
Sai dai wasu makusantan shugaban kasar sun nuna rashin jin dadinsu da faruwar lamarin ciki har da dan majalisar wakilai daga nan Kano Nasir Ali Ahmad da mataimakin shugaban kasa na musamman kan kafofin yada labarai Sha’aban Ibrahim Sharada, inda suka roki manema labarai a zauren da kada su yada labarin.
Wannan al’amari dai ya faru ne a yayin taron ganawa da shugaban kasa ya yi da al’ummar Najeriya mazauna Faransa da ma dalibai ‘yan asalin kasar nan da ke karatu a can.