Connect with us

Labarai

Tsoron rasa aiki ne ke hana jami’an gwamnati bai wa shugabannin siyasa shawarwarin gaskiya- Boss Mustapha

Published

on

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya yi gargaɗin cewa tsoron rasa aiki ko lalacewar makomar ma’aikata na iya hana jami’an gwamnati ba shugabannin siyasa shawarwarin gaskiya, lamarin da ka iya jefa shugabanni cikin manyan kura-kurai.

Mustapha ya ce jami’an da ke tsoron cewa faɗin gaskiya zai kawo musu cikas a aikinsu, za su iya zaɓar faɗin abin da shugabanni ke son ji, maimakon ba su shawarwarin ƙwararru da za su taimaka wajen tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.

 

Ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin gabatar da jawabin buɗe taron ƙungiyar tsofaffin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya da shugabannin ma’aikatan gwamnati na shekarar dubu biyu da ashirin da shida, mai taken rawar da ma’aikatan gwamnati ke takawa wajen tafiyar da mulki.

 

Tsohon sakataren, wanda ya riƙe muƙamin daga shekarar 2017 zuwa 2023 ya ce ƙarfin ma’aikatan gwamnati yana cikin iya ba da shawarwari na gaskiya, aiwatar da hukuncin da ya dace da doka da kuma bayyana sakamakon ayyukansu cikin gaskiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!