Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya yi maraba da ceto mutane 308 da aka sace su a jihohin Kwara da Neja

Published

on

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da ceto mutane 308 da aka sace a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Niger, tare da yabawa jami’an tsaro kan nasarar aikin.

 

A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, an ce daga cikin waɗanda aka ceto akwai mutane 163 daga al’ummar Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, da kuma 145 daga jihar Niger.

 

Sanarwar ta ce an ceto mutanen ne a dajin Kainji Lake National Park da ke ƙaramar hukumar New Bussa ta jihar Niger, bayan wani samame na haɗin gwiwa da cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa NCTC, Sojojin Najeriya, Hukumar Tsaro ta DSS da Rundunar ‘Yan Sanda suka gudanar bisa bayanan sirri.

 

Shugaba Tinubu ya yabawa jami’an tsaron bisa jajircewa da kyakkyawar haɗin gwiwa da suka nuna, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ayyukan tsaro ke ƙara inganta.

 

Haka kuma ya umarci hukumomin tsaro da su ƙarfafa hanyoyin samun bayanan sirri tun da wuri, da haɗin gwiwa da al’ummomi, tare da inganta matakan gaggawa domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare.

 

A halin yanzu, an ce mutanen da aka ceto na samun kulawar lafiya a sansanin soji na Wawa Cantonment, kafin a miƙa su ga gwamnatocin jihohinsu domin ci gaba da kula da su da kuma haɗa su da iyalansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!