Labarai
Shugaban Chadi Idriss Deby ya rasu
Shugaban Chadi Idriss Deby ya rasu.
Rasuwar tasa ta biyo bayan raunin da ya ji a bakin daga, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin kasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya bayyana
Deby ya rasu kwana guda da bayyana shi a matsayin wanda ya sake lashe zaben kasar karo na shida, kamar yadda sakamakon zaben da aka fitar na ranar Litinin ya bayyana.
Sakamakon ya nuna Deby mai shekaru 68, wanda ya hau karagar mulki a 1990, ya samu kashi 79.3 na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar na ranar 11 ga Afrilu.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Deby ya je bakin daga ne a karshen makon da muke ciki don ziyartar sojojin da ke yaki da ‘yan tawaye da ke kan iyakar Libya.
Ko a lokacin yakin neman zaben Deby ya alkawarta kawo zaman lafiya da tsaro a yankin.
You must be logged in to post a comment Login