Manyan Labarai
Shugaba Buhari ya kara wa’adin rufe iyakokin Najeriya .
Gwamnatin tarayya ta amince da ranar 31 ga watan janairun shekarar 2020 a matsayin ranar da zaa bude iyakokin Najeriya.
A wata sanarwa da mataimakin babban kwantrolla na hukumar hana fasakwauri ta kasa, Victor David Dimka ya sakawa hannu , ta yi kira ga wadanda abun ya shafa da su bi tsarin yadda ya kamata na ganin an bude iyakokin kasar nan cikin nasara.
Sanarwar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da cigaba da tsarin tsaftace iyakokin Najeriyar har zuwa 31 ga watan janairun shekarar badi.
An dai rufe iyakokin Najeriya tun ranar 20 ga watan Agustan shekarar bana ,sannan sanarwar ta hukumar hana fasakwaurin ta ce tana da yakinin ‘’yan kasuwa zasu karbi sanarwar da karfin gwiwa.
A ranar 20 ga watan Agusta ne shugaban hukumar hana fasakwauri ta kasa Kanal Hameed Ali mai ritaya ya sanar da aikin hadin gwiwa da jamian tsaron kasar nan, da ya hada da sojoji da ‘’yansanda da hukumar kula da shige da fice suka fara domin tsaftace iyakokin Najeriya ta kasa.