Labarai
Shugaban kasa ya yi afuwa ga wasu dattawa 3 a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga daya daga cikin dattawan kasar nan da suka yi fafutuka neman ‘yancin kai, marigayi, chief Anthony Enahoro da tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bendel, Farfesa Ambrose Ali.
Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da safiyar yau a birnin tarayya Abuja; yana mai cewa, a yanzu mutanen an wankesu daidai suke da wadanda kotuna ba su taba kama su da laifi a kotuna ba.
A cewar ministan, akwai wasu fitattun al’ummar kasar nan guda uku wadanda suma suka suka ci gajiyar afuwar ta Shugaban kasa.
Haka zalika ministan na cikin gida ya kuma ce, shugaba Buhari, ya kuma ba da umarnin sakin wasu fursunoni guda saba’in a gidan gyaran hali da ke Kuje a birnin tarayya Abuja, a matsayin wani mataki na rage cunkoson da ke gidajen gyaran hali a kasar nan.
Ogbeni Rauf Aregbesola ya kara da cewa, daukar wannan matakin ya biyo bayan shawarar da kwamitin shugaban kasa kan rage cunkoso a gidajen yarin kasar nan ya bayar.
AI
You must be logged in to post a comment Login