Addini
Shugaban NAHCON ya musanta bada umarnin kama Editan News Point

Shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya musanta zargin da jaridar News Point Nigeria ta wallafa cewa ya umarci jami’an tsaro su kama Editan ta.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai Ahmad Muazu, ya fitar a daren Talatar makon nan.
Sanarwar ta ce, labarin da aka wallafa, an kirkire shi ne domin bata sunan Farfesa Pakistan da kuma zubar da martabar hukumar da idon duniya.
You must be logged in to post a comment Login