Labarai
PDP tsagin Kabiru Turaki ta zargi APC da yin amfani da kalaman tunzura jama’a

Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki, ta zargi jam’iyya mai mulkin kasa APC da amfani da kalaman tunzura jama’a da kuma barazanar tashin hankali wajen neman ƙwace iko a siyasar ƙasar.
Ƙungiyar ta ce irin waɗannan kalamai na haifar da fargaba tare da zama babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
A cikin wata sanarwa, ɓangaren PDP ya yi Allah-wadai da abin da ya kira ƙoƙarin mayar da zaɓe tamkar yaki, yana mai cewa siyasa bai kamata ta zama hanyar haddasa zubar da jini ko razana ’yan ƙasa ba.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ’yan siyasa da jam’iyyun ƙasar da su guji kalaman da za su iya tayar da zaune tsaye, tare da mutunta tsarin dimokuraɗiyya da kuma bai wa al’umma damar zaɓar shugabanninsu cikin lumana.
Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tsaro da kuma yiwuwar tashin hankali gabanin zaɓen gwamnan jihar Osun da ke tafe.
You must be logged in to post a comment Login