Siyasa
Siyasa: APC ta kori Gudaji Kazaure
Jam’iyyar APC ta kori dan majisa mai wakiltar kananan hukumomin Kazaure, da Roni da Gwiwa da kuma Yan Kwashi ta jihar Jigawa daga jam’iyyar.
Kakakin jam’iyyar na mazabar Yamma dake Kazaure, Basiru Adamu Kazaure shi ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio.
Basiru Adamu ya ce dan majalisar ya gaza wajen yi musu ayyukan da suka zabe shi domin yi musu, sannan baya yin biyayya ga jam’iyya.
You must be logged in to post a comment Login