Connect with us

Labarai

Ƙarancin kuɗi da kayan aiki na ci gaba da kawo cikas ga ayyukan MNJTF a yankin tafkin Chadi

Published

on

Ƙarancin kuɗaɗe da kayan aiki na ci gaba da kawo cikas ga ayyukan Rundunar Haɗin Gwiwa ta ƙasashen yankin tafkin Chadi, MNJTF, wadda ke yaƙi da Boko Haram da ISWAP.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Najeriya ce ke ɗaukar babban kaso na kuɗaɗe, sojoji da kayan aikin rundunar, inda ta kashe kusan dala miliyan 209 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2021. Sai dai Tarayyar Turai ta ce ta bayar da tallafin Euro miliyan 234.4 ga rundunar, yayin da Birtaniya da Tarayyar Afirka su ma suka bayar da wasu tallafe.

 

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yi kira da ƙasashen Afirka da ke cikin rundunar su ƙara ɗaukar nauyin kuɗaɗen gudanar da ayyukanta, maimakon dogaro da tallafin ƙasashen waje. Masana tsaro kuma sun ce yaƙin ta’addanci ba zai tsaya kan amfani da ƙarfin soji kawai ba, inda suka buƙaci a magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da ƙarancin ilimi.

 

Rahoton ya kuma ce hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da haddasa mutuwar mutane da gudun hijira a yankin tafkin Chadi. Hukumar UNHCR ta ce sama da mutane miliyan 3.5 ne ke gudun hijira a yankin, yayin da Najeriya ke ɗauke da kashi 72 cikin 100 na mutanen da suka rasa muhallansu a ƙasashen da abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!