Labaran Wasanni
Sojin ruwa sun buga wasan Golf a Kano

Rundunar sojin ruwan Najeriya Navy ta gudanar da wasan Golf tsakanin Jami’an ta a Kano.
Wasan na zuwa ne a wani bangare na taron shekara da rundunar take gudanarwa a Kanon.
Yau Asabar 4 ga watan Satumbar shekarar 2021 ce dai ta kasan ce rana ta karshe da rundunar ta Kwashe tana gudanar da taron.
Rundunar sojin ruwan ta Navy ta fara taron a ranar Talata 31 ga watan Augusta inda ta karkare a yau 4 ga watan Satumba.
Wasan Golf din dai an gudanar da shi a filin wasa na Porto Golf dake garin Minjibir a kuma karamar hukumar ta Minjibir dake Kano.
You must be logged in to post a comment Login