Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Za a kafa kungiyar kwararrun ‘yan wasan Polo ta sojojin ruwan Najeriya

Published

on

Rundunar sojin saman kasar nan ta ce ta fara tantance jami’anta da suka kware wajen gudanar da wasan kwallon Polo, domin kafa kungiya ta musamman ta kwararru.

Babban hafsan sojin ruwan Najeriya (CNS), Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bikin rufe gasar Polo karo na 9 da aka gudanar a filin wasan Polo na Keffi, dake jihar Nassarawa.

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran rundunar na kasa Kwamado Sulaiman Dahun ya fitar ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta ce hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin wasannin Polo a Najeriya musamman tsakanin jami’an rundunar sojin ruwan.

Admiral Gambo ya ce “wasannin na Polo zai samar da hadin kai mai karfi tsakanin al’ummar kasar nan daban-daban tare da samar da zaman lafiya mai dorewa“.

Kazalika sanarwa ta ce shirya wasanni daban-daban tsakanin jami’an tsaron Najeriya zai kara haifar da hadin kai tsakanin su.

A cewar sa “ilimin kananan yara a Najeriya shine babban ci gaban da kasar nan take bukata a yanzu ta yadda zai saka a samu yaran da suke da ilimin da za su ci gaba da rike kasar nan“.

Ya kuma ce “domin haka ne ya sa rundunar sojin ruwan ta Najeriya za ta samar da karin tsaro da walwalar kanana yara da matasa a makarantun kasar nan”.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!