Connect with us

Labarai

An tsare fitacciyar ‘yar TikTok kan mutuwar saurayinta a Kano

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tsare fitacciyar ‘yar TikTok, Fati Cele, bayan rasuwar saurayinta, Isma’il Makaye, a gidanta da ke unguwar Danbare a Kano.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya janyo mutuwar.

Wata majiya ta bayyana cewa Fati Cele ta tada ƙarar neman taimako tana ikirarin cewa gobara ta tashi a gidanta, lamarin da ya sa aka kai Makaye Asibitin Nassarawa domin jinya, amma daga bisani ya rasu. Bayan faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda daga sashen Dorayi Babba suka tsare ta domin bincike, yayin da aka yi jana’izar marigayin, wanda ɗan kasuwar kayan kwalliya ne, bayan an miƙa gawarsa ga iyalansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!