Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga tare da ceto mutane 20

Published

on

Jami’an rundunar Sojin Nijeriya, na Operation Hadarin Daji, sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane tare da ceto wasu mutane 20 da suka sace a jihar Zamfara.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin na Operation Hadarin Daji Kaftin Ibrahim ya fitar a jiya Talata.

Kaftin Ibrahim, yace dakarun nasu sun sami nasarar ceto mutanan ne kimanin 20 ba tare da wani daga cikin su ya samu wani rauni ba ko kadan.

A cewarsa daga cikin wadanda suka hallaka akwai kasurgumin mai satar mutanan nan da ake kira da suna Sainaje.

Kaftin Ibrahim ta cikin sanarwar yace, dakarun Operation Hadarin Daji sun kai farmaki ne wani guri da ake kyautata zaton maboyarsu ce a Rukudawa,Dumburum, Tsanu, Birnin Tsaba, Magare da kuma Shamushelle dake Zurmi dukan su a karamar hukumar Birnin Magaji a jihar ta Zamfara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!