Labarai
Matafiyan da ke shigo wa daga kasashen da ke fama da Ebola na iya fuskantar cike fom- NCDC

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce, matafiya da ke shigowa kasar daga kasashen da ake fama da barkewar cutar Ebola, na iya fuskantar cike fom din bayyana bayanan lafiya.
NCDC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar gaggawa da ta fitar jiya Talata, yayin da ake ci gaba da samun barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Sanarwar da Darakta-Janar na hukumar, Dakta Jide Idris ya sanya wa hannu, ta ce matakin ya biyo bayan nazarin yadda cutar ke yaduwa da kuma tuntubar kwararrun kiwon lafiyar jama’a da ma’aikatar lafiya ta tarayya.
Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da gaggauta zuwa asibiti idan suka fara nuna alamomin da suka yi kama da na cutar Ebola.
You must be logged in to post a comment Login