Labarai
An ceto mutane 16 bayan rushewar wani gini a jihar Kano – Fire Service

Aƙalla mutane 16 ne aka ceto da ransu bayan rushewar wani ginin zama a Dan Dishe, Kwanar Yashi, da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano. Daga cikin waɗanda aka ceto, uku an tsamo su cikin halin suma.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:32 na safiyar Asabar, inda aka sanar da su game da rushewar ginin. Ya ce jami’an sun isa wurin, inda suka tarar da ginin mai girman ƙafa 20 da 30 ya rushe.
Hukumar kashe gobara ta ce an miƙa dukkan waɗanda abin ya shafa ga Usman Ibrahim, ɗan’uwan mahaifinsu, domin ci gaba da kula da su. A cewar hukumar, ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin rushewar, yayin da ta buƙaci jama’a da su ƙara taka-tsantsan, musamman a lokacin damina.
You must be logged in to post a comment Login