Labarai
DSS ta ƙara tsaurara matakan tsaro ga ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu

Hukumar tsaro ta DSS, ta ƙara tsaurara matakan tsaro ga ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya biyo bayan umarnin shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu na bai wa dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa kariya, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba.
Ya ce manufar matakin shi ne tabbatar da gudanar da yakin neman zaɓe cikin lumana, da kuma samar da yanayin da zai ba da damar gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci.
Daga cikin fitattun ‘yan siyasar da aka ƙarawa tsaron akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahoton ya ce DSS ta kuma faɗaɗa matakan tsaron zuwa ga ‘yan takarar gwamna da mataimakansu a faɗin ƙasar.
Haka kuma, wasu jihohi da ake ganin za su iya fuskantar rikici yayin zaɓe, an sanya su ƙarƙashin kulawa da sa ido na musamman.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke shirin fara yakin neman zabe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login