Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 21 tare da jikkata wasu

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarunta sun lalata wani sansanin ’yan ta’adda a yankin Kopre, da ke Karamar Hukumar Hong a Jihar Adamawa.

Rundunar ta ce aikin, wanda aka fara tun ranar Laraba, ya biyo bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’addan a yankin.

Ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda sama da 21 tare da jikkata wasu a yayin arangama daban-daban.

Haka kuma, sojojin sun lalata wasu muhimman kayayyakin ’yan ta’addan, ciki har da bindigar AK-47.

Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce hare-haren na daga cikin kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Mussa da Lassa.

Ya ce dakarun za su ci gaba da matsa lamba har sai an gano inda aka boye mutanen da aka sace tare da kubutar da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!