Labarai
Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Don Kuɓutar da Ƴan Uwansu da aka tsare a Kaduna
Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC a Nijeriya, ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami’an sojin saman ƙasar sun kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato ‘yan uwansu da hukumar ta tsare bisa zargin karya dokar aikin tsaro.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami’ain hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, jami’an EFCC suka kama wasu mutane biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke jihar Kaduna.
Hukumar ta ce ‘ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.
A yayin da ake tsare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattaunawa domin warware lamarin.
You must be logged in to post a comment Login