Addini
Sojojin Najeriya sun kashe kwamandojin Boko Haram 18 a jihar Borno
Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarunta da ke aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar nan, sun kashe wasu kwamandojin kungiyar boko haram da ISWAP su goma sha takwas a jihar Borno.
A cewar rundunar cikin kwamandojin boko haram da sojojin suka kashe har da Bukar Gana Fitchmeram da akewa lakabi da Abu Aisha.
Mai magana da yawun rundunar burgediya janar Muhammed Yerima ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce, ‘yan ta’addar sun fada komar dakarun sojin Najeriyar ne lokacin da suke kokarin kai wani harin ramuwar gayya a garin Damasak da ke jihar Borno.
You must be logged in to post a comment Login