Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu da Atiku ba su halarci taron sanya hannu kan Yarjejeniyar zaman lafiya ba

Published

on

‘Yan takarar shugabancin  ƙasa da wasu  jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Ƙasa domin gudanar da kamfen na zaɓen 2027 cikin lumana, tare da yin watsi da tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da tayar da zaune tsaye kan kabilanci ko addini.

 

Zaman ya gudana a birnin tarayya Abuja, a jiya Tallata  ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na ƙasa wato National Peace Committee (NPC) tare da haɗin gwiwar cibiyar  Kukah , wato Kukah Centre, gabanin fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a yau Laraba.

 

Sai dai wasu manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa, ciki har da ɗan takarar APC, Shugaba Bola Tinubu, da ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ba su halarci taron ba, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya wakilci Tinubu.

 

Daga cikin ‘yan takarar da suka halarta akwai Peter Obi na NDC, Adewole Adebayo na SDP da Omoyele Sowore na AAC.

 

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce yarjejeniyar ta zo a daidai lokacin da ya dace, da ya bayyana  cewa zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya zai gudana a 16 ga Janairu 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi zai gudana a 6 ga Fabrairu 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!