Ƙetare
Talabijin da Rediyo na Turkiyya ya ƙaddamar da sashensa na Hausa
Kafar yada labaran ƙasar Turkiyya TRT ta ƙaddamar da sabbin sassan yaɗa huɗu da za su rinka yada shirye-shiryensu a harsuna daban-daban.
Sabbin bangarorin sun haɗar da sashen Hausa da Swahili da Ingilishi da kuma Faransanci, sun kuma fara aiki Juma’ar nan.
Darakta janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci, ya ce za su mayar da hankali wajen yada shirye-shiryen da suka shafi nahiyar Afirka, a don haka ne suka ɗauki ma’aikata daga kasashe goma sha biyar na nahiyar.
Labarai masu alaƙa:
Turkiyya ta ɗebe ma’aikata 9 daga BBC Hausa
Wannan dai na cikin gagarumin shirin da Gidan Talabijin da Rediyo na Turkiya ya gudanar inda zai mayar da hankali kacokan kan nahiyar Africa, musamman masu amfani da harshen Hausa.
Gidan Talabijin da Rediyo na Turkiyya ya ɗauki ƙwararren mai kula da shafin BBC Hausa Nasidi Adamu Yahaya a matsayin shugaban sashen Hausa na Turkiyya.
Ya kuma ɗaukar masa ƙwararrun mataimaka biyu da suka hada da Halima Umar Saleh wadda fitacciyar mai gabatar da shirye-shiryen intanet irinsu “Zamantakewa” da kuma Ishaq Khalid ƙwararren mai rahoton BBC cikin harsunan Hausa da Turanci.
You must be logged in to post a comment Login