Labarai
Talauci da halin matsin rayuwar da yan Nijeriya ke ciki na da alaka da rashin adalci- Amnesty
Kungiyar kare hakkin Bil-adama ta Amnesty International, ta ce, talauci da halin matsin rayuwar da al’ummar Nijeriya ke ciki na da alaka da rashin adalci da rashin kula da hakkin talakawa daga shugabanni.
Shugaban kungiyar na Najeriya Isah Sunusi, ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da masana da yan jarida kan hakkin da Bil-adama ke da shi da kungiyar ta shirya.
Isah Garba ya kuma ce rashin sanin hakki da yancin kan da yan kasar nan basu yi ba shine ya sanya kungiyar ta yi wani jadawali da ya fayyace hakkokin da kuma mafita ta mikawa gwamnati,kuma kungiyar ta shirya yadashi ga alumma don rage matsalolin cin zarafi da cin hanci da rashawa.
Shi ma da ya kasance a wajen taron Dakta Sulaiman Yar aduwa malami a tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero ta Kano, ya ce, yan jarida na taka rawa wajen ankarar da gwamnati da kuma ilmantar da mutane hakkin su dake a kan gwamnati ta yadda zasu rika bibiyar hakkokinsu.
A nasa bangaren shugaban kungiyar nan dake sanya idanu kan ayyukan majalisun dokokin kasa da yaki da cin hanci da rashawa ta CISLAC Dakta Auwal Musa Rafsanjani ya bayyana cewa, Rashin mayar da hankali da hukumomi ke yi tare da nuna halin ko in kula wajen daukar matakin da ya kamata ga yan ta’addan da ke aikata ta addanci kan mutane ne ke kara ta’azzara matsalar tsaro.
Ya Kuma ce dole ne sai yan Jarida sun tashi tsaye wajen yada irin matsalolin ta addancin da ake yi wa kananan yara da ‘ya’ya mata a Najeriya domin dakile matsalar.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login