Labaran Kano
Tallafawa marayu na rage radadin rashin iyaye
Wata kungiya dake tallafawa wadanda aka ci zarafinsu, marayu da kuma marasa galihu mai suna ISSOL, ta shawarci al’umma dasu rinka taimakon marayu da raunana tare da jansu a jiki don rage musu radadin da suke ciki na rayuwa.
Shugabar kungiyar Barista Sadiya Adamu Aliyu ce ta bayyana haka yayin rabon kayan tallafin karatu da kungiyar tayi a makarantar marayu da raunana ta Darul Yateem dake unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni a nan kano.
Ta kara da cewa kamata yayi mawadata a cikin al’umma su rinka bude irin wadannan makarantun da zasu rinka ilmantar da marayu da marasa galihu don bunkasa iliminsu kamar sauran yara masu galihu.
A nasa bangaren wacce ta assasa makaranta Malama Fatima Abdullahi ta bayyana cewa makasudin bude makaranta shine don ilmantar da marayu da kuma raunana inda tayi kira ga Gwamnatin jihar kano dasu taimakawa makarantar da karin a zuzuwa tare da samarwa da mata mazauni na dindindin.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa kungiyar ta ISSOL ta raba kayan karatu da kayan abinci ga iyayen yara da malam makarantar ta Darul Yateem.