Labaran Wasanni
Tammy Abraham zai bugawa kasar Ingila wasa sabanin Nijeriya
Biyo bayan kin bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila Tammy Abraham cikin jerin sunayen da zasu wakilci Nigeria, mai haras da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa kasar Ingila Gareth Southgate ya sanya sunan dan wasan cikin ‘yan wasan da zasu wakilci kasar ta Ingila a wasannin da zata fafata a kwanannan.
Tammy Abraham dai yana da damar ya zabi kasar kasar da zai bugawa wasa tsakanin Nijeriya da Ingila, sai da mai horas da ‘yan wasan Nigeria Gernot Rohr yace a yanzu haka Nijeriya bata bukatar dan wasan.
Dan wasan mai shekaru 22 yanzu haka ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kwallaye 7 a wasanni 7 da ya buga a gasar Primiyar kasar Ingila a kakar wasanni ta bana.
Nijeriya dai tana fama da matsalar ‘yan wasan gaba biyo bayan ritaya da Odion Ighalo ya yi.
Sai dai har yanzu Gernot Rohr bai gama gamsuwa da yadda Abraham ke taka leda ba, a don haka yake ganin yanzu Nijeriya tana da manyan ‘yan wasa wadanda suka fi Tammy Abraham iya wasa.