Labaran Kano
Tarihin Marigayi Abdulƙadir Abubakar Rano DPO na Jibiya da ƴan bindiga suka kashe
Marigayin DSP Abdulƙadir Abubakar Rano ɗan asalin ƙaramar hukumar Rano ne kuma an haife shi a garin na Rano da ke kano, kuma shi ne DPO na yankin Jibiya kafin rasuwarsa sanadiyyar harin ƴan bindiga a Katsina.
An dai haifi Abdulƙadir Abubakar Rano wanda ake kira da (Baballiya) a shekara ta 1978 a garin Rano in da yayi karatun sa na firamare a cikin garin haka zalika ya halaccin makarantar Gwamnati ta sakandare da ke garin na Rano.
Bayan kammala karatun sakandaren nashi ya dawo cikin birnin kano inda ya halacci wata makaran mai zaman kanta inda yayi diploma a makarantar bayan nan ya ƙara ci gaba da karatun in da yayi babbar diploma HND.
Bayan kammala karatun na sane ya sami gurbi a hukumar ƴan sanda a shekara ta 2006 kuma ya kama aiki a shekarar, a cikin aikin nashi ne yasa ya dunga zuwa karin karatu a ƙarƙashin hukumar ƴan sanda inda yakai har izuwa wannan matsayi da yake kafin rasuwar tashi.
Haka kuma ya gudanar da aikin sa a sassa daban-daban na ƙasar nan inda daga ƙarshe ya riƙe muƙamin DPO a garin Jibiya ta jihar Katsina.
A zantawar da Freedom Radio ta yi da mahaifiyar mamacin Hajiya Maryam Abubakar Rano ta ce wannan ba ƙaramin rashi tayi ba domin kuwa ya kasan ce jajirtacce a cikin ƴan uwansa.
DSP Abdulƙadir Abubakar ya rasu yana da shekaru arba’in da hudu in da ya bar mahaifiyar sa da Mata ɗaya sai ƴaƴa uku.
You must be logged in to post a comment Login