Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Tarihin marigayi Muhammad Adamu Dankabo

Published

on

An haifi marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan kabo a ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 1942 a karamar humar Kabo ta jihar Kano.

Inda yayi karatun Al’qurani a garin Kabo ya fara karatun firamare a garin gwarzo daga nan ya samu gurbin karatu a makarantar lardi dake Kano.

Marigayin ya halarci makarantar horar da aiki jirgin sama ta FTC Kaduna da ta kwaleji B O C da ke kasar Amurka.

Ya samu shaidar difloma ta harkoki kasuwancin sufuri jiragen sama kuma ya sha gwagwarmaya da dama a fannin aikin daga cikin gida zuwa kasashen ketare tun daga matsayin me kula da jirgi har ya zamo mai bada abinci ya kuma kai ga matakin mallakar jirgin kansa da kamfanin sa na Kabo Air.

Jarman Kano Adamu Dankabo ya fito da sunan jihar Kano dama Najeriya baki ɗaya a harkar sufurin jirgin sama, saboda wannan hidima tare da gwagwarmaya wacce Dankabo ya yi, ya sanya mai marigayi martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya naɗa shi sarautar Jarman Kano na farko a daular fulanin Kano.

Ya kuma ba shi aikin kulawa da sabuwar gundumar ƙaramar hukumar Kabo da aka kirkiro daga gundumar Gwarzo wanna aiki yayi har Allah ya kari kwanansa a ranar 4 ga watan Aprilun shekarar 2002.

Jarman Kano ya shahara wajen aikin alheri da ya mamaye dukkan jama’ar zamaninsa saboda irin halin sa na baiwar kyauta. Ya samu sarautu da dama a sassan faɗin ƙasar nan, waɗanda su ka haɗar da; Sardaunan Kagoro, Galadiman Pankshin, Ida Idaha Ke Iburutu na Kalaba.

Muhammad Dankabo ya rasu ya bar iyalin sa da dama, cikin ya’yansa kuwa akwai Hajiya Asiya ta ce “Mahaifinmu yana da kyakyawar alaka da mu, kuma yana dauko yaran yan uwa ya rike su tamkar nasa.

Yana da raha barkwanci, abinsa bai rufe masa ido ba, domin kuwa yana da kyauta, kuma yana son yaga al’umma sun samu ci gaba” a cewar Hajiya Asiya.

Shi ma Auwal Isa Kabo Majidadin Kabo kuma guda daga cikin wadanda suka yi aiki a kamfanin Kabo Air ya ce “Nayi aiki sama da shekara 14 a kamfaninsa, yana da mu’amala ba zaka gane shi ne mamallakin wajen ba kuma duk shekara yana biya mana aikin Hajji baya ga albashi da alawus da yake ba mu”.

Alhaji Miko Nuhu shi ne shamakin marigayi Dankabo ya ce “Baya gajiya da kyauta, ko shekarar da zai rasu sai da sayi gero tirela 2 ya raba kananan hukumomi 6 na jihar Kano, kuma baya son a ambaci sunansa in ya bada kyauta”.

Marigayi Jarman Kano Alhaji Muhammad Adamu Dankabo ya rasu aranar 4 ga watan Afrilun shekarar 2002 yana da shekara 60.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!