Labarai
Taron zauren MDD: Muna fatan a kawo ƙarshen matsalar wariyar launin fata a Afurka – Buhari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan matsalar wariyar launin fata da ake ci gaba da fuskanta a faɗin duniya.
Wannan na zuwa ne duk da ci gaban da aka samu a ɓangarori daban-daban na rayuwa.
Shugaban ya bayyana hakan a Juma’ar nan yayin jawabinsa a taron zauren majalisar dinkin duniya karo na 76.
“Matsalar wariyar launin fata na taka mummunar rawa wajen aikata miyagun laifuka, musamman ga al’ummar da suka fito daga nahiyar Afirka” a cewar Buhari.
Buhari ya kuma ce, “Sakamakon wannan matsala, ina fatan wannan zaure, zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan ta, domin kuwa babbar matsala ce da ta ke illa ga waɗanda suka tsinci kansu a ciki musamman a kasata Najeriya, mun dade muna yaki da wannan mummunar ta’ada wadda a yanzu take sabbaba matsaloli masu tarin yawa”.
Haka kuma ya ce, a halin yanzu ya zame wajibi a matsayin su na shugabanni su zage dantse wajen yaƙi da annobar COVID-19 don ganin cewa al’umma sun samu waraka tare da dakile cigaba da yaɗuwarta.
“Wannan zaure, da ke tattara kasashe don warware ƙalubalen da ake fuskanta yanzu haka a fadin duniya don haka Najeriya ta yi imanin cewa majalisar ɗinkin duniya za ta ƙara azama don ci gaba da aiki tare da dukkan ƙasashe membobinta don ƙara inganta fannonin da suka shafi zaman lafiya da tsaro, tare da ci gaba da kare hakkin dan adam” a cewar Buhari.
“Kazalika ina ƙarƙare wannan jawabi da yin fatan alheri ga Angela Markel shugabar gwamnatin Jamus da ke dab da sauka daga mulki” Buhari ya ƙara da cewa.
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo ƙasar nan a ranar Lahadi bayan kammala babban taron zauren Majalisar ɗinkin duniya karo na 76.
You must be logged in to post a comment Login