Labarai
Tashar freedom rediyo na wayar da kan mutane –Sarkin Alkalman Kano
Sarkin Alkalman Kano Alhaji Iliyasu Labaran Daneji ya bayyana gidan Redio Freedom a matsayin daya tilo a Arewacin Najeriya dake koyar da kowane fanni daya shafi rayuwar dan Adam musamman wajen wayar da kan mutane su san hakkinsu.
Alhaji Iliyasu Labaran Daneji ya bayyana hakan ne a wani bangare na taya gidan radio Freedom murnar bikin cikarta shekaru goma sha shida da kafuwa.
Sarkin Alkalma ya kuma kara da cewa Redio Freedom tazama tamkar mudubin sauran kafafen yada labarai a Arewacin kasar nan wajen koyon shirye shirye masu amfani ga jama’a domin warware musu matsalolin su kai tsaye harma da Ilmantarwa fadakarwa da nishadantarwa.
Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun Freedom Radio
Freedom Radio za ta buga wasan sada zumunci da Road Safety
Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun Freedom Radio
Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya nanata cewa babban abunda ya daukaka gidan Radio Freedom bai wuce yadda ma’aikatanta suka mayarda hankali wajen nemawa marasa lafiya tallafi domin neman lafiyarsu , don haka suna rokon Allah ya cigaba da tallafawa gidan ya kuma cigaba da daukakashi a idon duniya.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Sarkin Alkalman Kano Iliyasu Labaran Daneji na fatan Radio Freedom zasu cigaba da rike kambun su musamman wajen gudanarda shirye shiryen da suka shafi jama’a kai tsaye.