Kiwon Lafiya
Tashin hankalin da aka shiga a Libya na daga cikin dalilan samun tashin hankali a Najeriya-shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, tashin hankalin da aka shiga a kasar Libya na daya daga cikin dalilan da suka sa ake samun tashin hankali a Najeriya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da gidan rediyon Muryar amurka inda ya ce hakan ce ta tilastawa makiyaya dake yawo da sanda suka fara daukar bindiga.
Shugaba Buhari ya ce duk da cewa al’umma na alakanta rikicin Fulani da Makiyaya da kabilanici da kuma addini, amma a zahirin gaskiya wahalar da ake samu na da alaka da shigowar mutane daga kasashen ketare musamman ma kasar libiya
Shugaban kasar ya kuma ce barnar da aka yiwa tsarin da magabatan shugabannin irinsu Sardauna suka yi wadanda suka samar da burtaliai ga makiyaya, aka yi dam-dam aka kuma sa famfo mai amfani da iska, wadanda masu hali suka dauka suka maida manyan gonakin su , ya zama sanadin matsalar da ake ciki yanzu.
Ya kara da cewa, mutanen da ake kashewa a Zamfara sun fi wadanda ake kashewa a Taraba da Benuwe yawa, amma sai a rika cewa, sha’ainin addini ko kabilanci ne yak e faruwa.