Connect with us

Labarai

Tinubu ya buƙaci a bai wa Afirka kujerun dindindin guda biyu a MDD

Published

on

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a bai wa nahiyar Afirka kujerun dindindin guda biyu a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da ƙarin kujeru biyar na wucin gadi .

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya gabatar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da Yake gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban ya ce bai kamata a ci gaba da barin Afirka a wajen tsarin kujerun dindindin na kwamitin ba, duk da irin nauyin da nahiyar ke ɗauka wajen fuskantar rikice-rikice. Ya kuma buƙaci a bai wa Afirka cikakken haƙƙin zama mamba na dindindin.

Tinubu ya kuma yi kira da a sauya tsarin kuɗaɗen duniya domin rage wa ƙasashe masu tasowa nauyin bashi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta’addanci da kuma warware rikice-rikice ta hanyar diflomasiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!