Labarai
An sake kwaso ’yan Najeriya 105 daga Afirka ta Kudu

Wasu ’yan Najeriya 105 sun sake dawowa gida daga Afirka ta Kudu, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa game da tsaron ’yan ƙasashen waje gabanin wa’adin 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka ayyana.
Mutanen sun isa birnin Lagos cikin jirgin South African Airways da misalin ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar nan ta bayyana.
Ma’aikatar ta shaida wa BBC yau Juma’a cewa gwamnati ta taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya 1,821 tun daga watan Yuni, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin sake ɓarkewar hare-hare kan baƙi da ’yan Afirka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Femi Adeniyi, ya ce Ana ci gaba da ƙoƙarin kwaso ƙarin ’yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali sakamakon fargabar tsaro a Afirka ta Kudu.”
You must be logged in to post a comment Login