Labarai
Shugaban KH Bungudu ta Zamfara da wasu mutane sun kuɓuta a hannun masu garkuwa da mutane

Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara da wasu mutane huɗu sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa mutane
Shugaban ƙaramar hukumar Nura Abdullahi, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutanen ne bayan shafe kwanaki 61 a hannun yanbindigar.
Rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaranta, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Alhamis a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce Mista Nura Abdullahi da wasu mutane huɗu sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutanen ne a yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar.
An yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar ne a ranar 25 ga watan Yulin 2026, bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansa da ke garin Bungudu.
Rundunar ta ce an karɓi mutanen da suka kuɓuta kuma ana ba su kulawar da ta dace, kafin daga bisani a mika su ga iyalansu.
You must be logged in to post a comment Login