Labarai
Yau za a yi Sallar Gani a Kano karon farko a tarihin Masarautar Jihar

A yau ne Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu zai gudanar da hawan sallar gani a cikin birnin Kano wanda zai kasance karo na farko a tarihin Masarautar Kano.
Rahotanni daga fadar Sarkin sunce za’a gudanar da hawan ne a yau Asabar da kuma gobe Lahadi inda Mai Martaba Sarkin zai fito domin halartar bukukuwan hawan sallar gani.
Hawan sallar gani wata al’ada ce da ake gudanarwa a wasu masarautun arewacin Najeriya.
Anasa ran wannan hawan sallar gani gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai kasance babban bako a yayi hawan.
Hawan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye shiryen bukukuwan Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Ku kasance da mu a shafin mu na Facebook a FreedomradioNigeria domin kallan hawan kai tsaye da kuma sauraro tashoshin mu wato Freedom Radio da Dala fm a yammacin wannan rana.
You must be logged in to post a comment Login