Labarai
Mutane 10,000 ne suka kamu da cutar mashaƙo a 2026- NCDC

Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce sama da mutane 10,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar mashaƙo a 2026.
Darakta-Janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a wani taron manema labarai kan halin da ake ciki game da barkewar cutar kwalara da mashaƙo a Najeriya.
Sai dai Dakta Idris ya ce an samu raguwar masu kamuwa da cutar kwalara a farkon shekarar nan, idan aka kwatanata da 2025.
Dakta Idris ya ce an samu rahoton sama da mutum 65,000 da ake zargin sun kamu da kwalara a jihohi 35 da kuma kusan ƙananan hukumomi 195 a bana, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Dakta Idris ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan dakile barkewar cututtukan.
You must be logged in to post a comment Login