Connect with us

Labarai

Hisbah ta gargaɗi ɗalibai kan aikata baɗala da sunan murnar kammala karatu

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi gargaɗi ga ɗaliban da ke shirin kammala karatunsu na makarantun sakandare a cikin makon nan da su guji aikata baɗala ko gudanar da ayyukan da suka saɓa wa tarbiyya da sunan shagulgulan kammala karatu.

 

Hukumar ta kuma yi kira ga ɗaliban da su guji sanya launuka ko rubuce-rubuce a jikin kayan makarantarsu da ka iya tauye martabar makaranta ko kuma karya ƙa’idojin tarbiyya.

 

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa Freedom Radio.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!