Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: ba ni da alaka da wata kungiyar ta’addanci – Janar Abdussalami Abubakar

Published

on

Tsohon shugaban mulkin soji na kasar nan Janar abdussalami Abubakar mai ritaya ya musanta zargin cewa yana da alaka da wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da wasu ‘yan tadda da ke aikata ta’addanci a jihar Niger.

 

Tsohon shugaban mulkin sojin na Najeriya ya bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege da aka shirya don bata masa suna.

 

A cikin wata sanarwa da tsohon shugaban kasar ya fitar  mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Dr. Yakubu Suleiman, ta ce, labarin da wasu kafafen yada labarai su ka yi da ke cewa an kama wani jirgin shalkwabta da ke rarraba abinci da makamai ga ‘yan bindiga a jihar ba gaskiya bane.

 

Sanarwar ta ce labarin ba gaskiya bane kuma tsohon shugaban kasar ba shi da alaka da wata kungiya ta ta’addanci.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!