Labarai
Tsaro : Ganduje ya shawarci Buhari da’a hana fulani makiyya na ketare zuwa Najeriya
Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci gwamnatin tarrayya da ta hana fulani makiyya na kasashen ketare zuwa Najeriya kasancewar ana samun karuwar rashin tsaro a Najeriya.
Abdullahi Umar Ganduje ya ce bai dace a dinga kiran fulani makiyya a matsayin ‘yan ta’adda ba.
Yana mai cewa, da ya daga cikin fulani makiyya na gudanar da sana’ao’in su na kiwon dabbobi wanda hakan ke bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa musu
Gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a tattaunawar sa da sashin Hausa na gidan Rediyo Faransa RFI, yana mai cewa gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-R rufa’i bai fahimci kokarin da gwamnonin Arewa ke yi ba wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewacin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login